Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Mafari

Littattafan Bishara gefe da gefe · Mafari

Baftismar Yesu

Mat 3:13–17 · Mar 1:9–11 · Luk 3:21–22 · Yoh 1:29–34

Mattiyu

Mat 3:13–17

13Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma.

14Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?”

15Yesu ya amsa ya ce, “Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.” Sa’an nan Yohanna ya yarda.

16Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa.

17Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”

Markus

Mar 1:9–11

9A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun.

10Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya.

11Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.”

Luka

Luk 3:21–22

21Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe,

22Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”

Yohanna

Yoh 1:29–34

29Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!

30Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’

31Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”

32Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.

33Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

34Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY