Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Gicciye Yesu

Mat 27:32–44 · Mar 15:21–27, 29–32 · Luk 23:26–43 · Yoh 19:17–27

Mattiyu

Mat 27:32–44

32Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.

33Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).

34A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.

35Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.

36Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.

37Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

38An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.

39Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,

40suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

41Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

42“Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

43Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

44Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

Markus

Mar 15:21–27, 29–32

21Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen.

22Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).

23Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba.

24Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

25Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.

26Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.

27Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

29Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku,

30sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

31Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa!

32Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

Luka

Luk 23:26–43

26Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.

27Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa.

28Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku.

29Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’

30Sa’an nan “ ‘za su ce wa duwatsu, “Ku fāɗi a kanmu!” Za su ce wa tuddai kuma, “Ku rufe mu!” ’

31Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?”

32Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye.

33Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

34Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

35Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

36Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.

37Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

38Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

39Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”

40Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?

41Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

42Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”

43Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

Yohanna

Yoh 19:17–27

17Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota).

18Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.

19Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.

20Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik.

21Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”

22Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”

23Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.

24Sai suka ce wa juna, “Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce, “Suka rarraba tufafina a junansu, suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata.” Abin da sojojin suka yi ke nan.

25To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin.

26Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,”

27ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY