Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Mutuwar Yesu

Mat 27:45–56 · Mar 15:33–41 · Luk 23:44–49 · Yoh 19:28–30

Mattiyu

Mat 27:45–56

45Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.

46Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

47Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”

48Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha.

49Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

50Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

51A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe.

52Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.

53Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

54Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

55Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima.

56A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.

Markus

Mar 15:33–41

33Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar.

34A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

35Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”

36Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”

37Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.

38Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa.

39Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”

40Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf, da kuma Salome.

41A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.

Luka

Luk 23:44–49

44Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara,

45domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu.

46Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.

47Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.”

48Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi.

49Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan.

Yohanna

Yoh 19:28–30

28Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”

29To, akwai wani tulun ruwan tsami ajiye a can, saboda haka suka jiƙa soso da shi, suka soka soson a sandan itacen hizzob, suka kai bakin Yesu.

30Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY