Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Tashin Yesu daga matattu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Tashin Yesu daga matattu

Yesu ya bayyana ga almajirai

Luk 24:36–49 · Yoh 20:19–23

Luka

Luk 24:36–49

36Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”

37Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.

38Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?

39Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

40Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

41Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?”

42Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,

43ya karɓa ya ci a gabansu.

44Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”

45Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.

46Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.

47Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.

48Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

49Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”

Yohanna

Yoh 20:19–23

19Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama tă kasance tare da ku!”

20Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.

21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama tă kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.”

22Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki.

23Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY