Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 7

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 7, 2027

Lahadi · Mako na 5 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Lahadi ta 5 ta lokacin yau da kullum

Lahadi · Launin ibada: kore

Karatun yini

Karatu na farko

Ayu 7:1–4, 6–7

1“Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne? 2Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi. 3Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu. 4Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe. 6“Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege. 7Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba.

Zaburar amsawa

Zab 147:1–6

1Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi! 2Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta. 3Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu. 4Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna. 5Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka. 6Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

Karatu na biyu

1Kor 9:16–19, 22–23

16Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba! 17In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. 18To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba. 19Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 22Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.

Bishara

Mar 1:29–39

29Da suka bar majami’ar, sai suka tafi gidan su Siman da Andarawus, tare da Yaƙub da Yohanna. 30Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. 31Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima. 32A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. 33Duk garin ya taru a ƙofar gidan. 34Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi. 35Da sassafe, tun da sauran duhu, Yesu ya tashi, ya bar gida, ya tafi wani wurin da ba kowa, a can ya yi addu’a. 36Siman da abokansa suka fita nemansa. 37Da suka same shi, sai suka ce, “Kowa yana nemanka!” 38Yesu ya amsa ya ce, “Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.” 39Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi