Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Faburairu 2027 › Faburairu 8

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Faburairu 8, 2027

Litinin · Mako na 5 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Litinin a mako na 5 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Waliyyi Jerome Emiliani, firist · Tunawa da ba dole ba

Waliyya Josephine Bakhita, budurwa · Tunawa da ba dole ba

Karatun yini

Karatu na farko

Far 1:1–19

1A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. 2To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. 3Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. 4Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. 5Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan. 6Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” 7Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. 8Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan. 9Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. 10Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. 11Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. 12Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. 13Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan. 14Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, 15bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. 16Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. 17Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, 18su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.

Zaburar amsawa

Zab 104:1–2, 5–6, 10–12, 24, 35

1Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka. 2Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti 5Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba. 6Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu. 10Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu. 11Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu. 12Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa. 24Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka. 35Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.

Bishara

Mar 6:53–56

53Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. 54Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. 56Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi