Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda
Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda
Dawuda ya ci Urushalima
2Sam 5:6–10 · 1Tar 11:4–9
2Sam 5:6–106Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”
7Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.
8A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”
9Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.
10Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi.
1Tar 11:4–94Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin
5suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.
6Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.
7Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda.
8Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin.
9Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi.
An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY