Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Shawulu da Dawuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Shawulu da Dawuda

Hiram ya gina wa Dawuda fada; ’ya’yan Dawuda maza

2Sam 5:11–16 · 1Tar 14:1–7

2 Sama’ila

2Sam 5:11–16

11To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.

12Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya naɗa shi sarki bisa Isra’ila, ya kuma ɗaukaka masarautarsa saboda mutanensa Isra’ila.

13Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata.

14Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,

15Ibhar, Elishuwa, Nefeg, Yafiya,

16Elishama, Eliyada da Elifelet.

1 Tarihi

1Tar 14:1–7

1To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da ’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada.

2Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila.

3A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin ’ya’yan maza da mata.

4Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,

5Ibhar, Elishuwa, Elfelet,

6Noga, Nefeg, Yafiya,

7Elishama, Beyeliyada da Elifelet.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY