Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

Manzanni goma sha biyu

Mat 10:1–4 · Mar 3:13–19 · Luk 6:12–16

Mattiyu

Mat 10:1–4

1Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

2Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu, da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;

3Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;

4Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.

Markus

Mar 3:13–19

13Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.

14Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi,

15don kuma su sami ikon fitar da aljanu.

16Ga sha biyun da ya naɗa. Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);

17Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);

18Andarawus, Filibus, Bartolomeyu, Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Taddayus, Siman wanda ake kira Zilot,

19da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

Luka

Luk 6:12–16

12Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah.

13Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.

14Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus, Yaƙub, Yohanna, Filibus, Bartolomeyu,

15Mattiyu, Toma, Yaƙub ɗan Alfayus, Siman wanda ake kira Zilot,

16Yahuda ɗan Yaƙub, da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY