Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Koyarwa

Littattafan Bishara gefe da gefe · Koyarwa

Misalin mai shuka

Mat 13:1–9 · Mar 4:1–9 · Luk 8:4–8

Mattiyu

Mat 13:1–9

1A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin.

2Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci.

3Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, “Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.

4Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su.

5Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi.

6Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai.

7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su.

8Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.

9Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Markus

Mar 4:1–9

1Har wa yau, Yesu ya fara koyarwa a bakin tafki. Domin taron da yake kewaye da shi mai girma ne sosai, sai ya shiga cikin jirgin ruwa, ya zauna a ciki a tafkin, dukan mutanen kuwa suna a gaɓar ruwan.

2Ya koya musu abubuwa da yawa da misalai. A koyarwarsa kuwa ya ce,

3“Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.

4Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su.

5Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi.

6Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa.

7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba.

8Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”

9Sai Yesu ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Luka

Luk 8:4–8

4Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce,

5“Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.

6Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin.

7Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.

8Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.” Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY