Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

An warkar da shanyayye

Mat 9:1–8 · Mar 2:1–12 · Luk 5:17–26

Mattiyu

Mat 9:1–8

1Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.

2Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

3Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

4Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?

5Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’

6Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

7Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.

8Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

Markus

Mar 2:1–12

1Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida.

2Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara.

3Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye.

4Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa.

5Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.”

6To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa,

7“Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

8Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa?

9Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’?

10Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen,

11“Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”

12Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”

Luka

Luk 5:17–26

17Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo.

18Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu.

19Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.

20Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, “Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

21Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

22Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?

23Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?

24Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

25Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.

26Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY