Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Galili

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Galili

An tsabtacce mutum mai kuturta

Mat 8:1–4 · Mar 1:40–45 · Luk 5:12–16

Mattiyu

Mat 8:1–4

1Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.

2Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”

3Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.

4Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”

Markus

Mar 1:40–45

40Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.”

41Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka tsabtacce!”

42Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.

43Yesu ya sallame shi nan take, da gargaɗi mai ƙarfi cewa,

44“Ka lura kada ka gaya wa kowa wannan. Amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayun da Musa ya umarta saboda tsarkakewarka, don yă zama shaida gare su.”

45A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.

Luka

Luk 5:12–16

12Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.”

13Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, “Na yarda, ka zama da tsabta!” Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.

14Sai Yesu ya umarce shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa, amma ka tafi ka nuna kanka ga firist, ka kuma miƙa hadayu da Musa ya umarta, saboda tsarkakewarka ta zama shaida a gare su.”

15Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.

16Amma Yesu sau da yawa, yakan keɓe kansa zuwa wuraren da ba kowa, yă yi addu’a.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY