Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Binne Yesu

Mat 27:57–61 · Mar 15:42–47 · Luk 23:50–56 · Yoh 19:38–42

Mattiyu

Mat 27:57–61

57Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.

58Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.

59Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta.

60Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa.

61Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.

Markus

Mar 15:42–47

42Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai

43Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

44Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.

45Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.

46Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.

47Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.

Luka

Luk 23:50–56

50Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci,

51shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah.

52Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.

53Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba.

54An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa.

55Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.

56Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.

Yohanna

Yoh 19:38–42

38Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.

39Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari.

40Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza.

41A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba.

42Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY