Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Barabbas, da hukuncin

Mat 27:15–26 · Mar 15:6–15 · Luk 23:13–16, 18–25 · Yoh 18:39–40; 19:1–16

Mattiyu

Mat 27:15–26

15A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa.

16To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.

17Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”

18Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.

19Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”

20Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.

21Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”

22Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”

23Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”

24Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

25Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”

26Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

Markus

Mar 15:6–15

6Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.

7Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.

8Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.

9Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

10Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.

11Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

12Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”

13Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

14Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”

15Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

Luka

Luk 23:13–16, 18–25

13Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane,

14ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba.

15Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa.

16Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.”

18Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!”

19(Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)

20Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu.

21Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”

23Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.

24Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.

25Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu.

Yohanna

Yoh 18:39–40; 19:1–16

18:39Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”

18:40Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.

19:1Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.

19:2Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.

19:3Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.

19:4Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.”

19:5Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”

19:6Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”

19:7Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”

19:8Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,

19:9sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.

19:10Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”

19:11Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”

19:12Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”

19:13Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata).

19:14Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”

19:15Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”

19:16A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY