Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima

Kwanakin matsananciyar wahala

Mat 24:15–28 · Mar 13:14–23 · Luk 21:20–24

Mattiyu

Mat 24:15–28

15“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’ wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),

16to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.

17Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.

18Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa.

19Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!

20Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.

21Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.

22“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.

23A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.

24Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.

25Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.

26“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.

27Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.

28Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.

Markus

Mar 13:14–23

14“Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’ tsaye inda bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.

15Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu.

16Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa.

17Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!

18Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.

19Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.

20“Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.

21A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.

22Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.

23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.

Luka

Luk 21:20–24

20“In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.

21A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.

22Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.

23Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.

24Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY