Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Amincin Allah
Bangaskiya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Amincin Allah
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (12), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
1Yoh 1:9
In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.2Tim 2:13
in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”Ibr 10:23
Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.Mako 3:22–23
Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.M Sh 7:9
Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.2Tes 3:3
Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.1Kor 10:13
Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.1Kor 1:9
Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.Zab 91:4
Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.Zab 36:5
Ƙaunarka, ya Ubangiji, kan kai sammai, amincinka har sararin sammai.1Bit 4:19
Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.1Tes 5:24
Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.