Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Manufar rayuwa

Bangaskiya

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Manufar rayuwa

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (12), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

Rom 8:28Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.
Afi 2:10Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
M Had 12:13–14Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.
Zab 138:8Ubangiji zai cika manufarsa a kaina; ƙaunarka, ya Ubangiji, madawwamiya ce har abada, kada ka ƙyale ayyukan hannuwanka.
K Mag 16:9’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
1Bit 2:9Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.
Rom 12:2Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Irm 1:5“Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”
Zab 20:4Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
1Kor 10:31Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Zab 37:5Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
Ish 43:7kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.