Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Alkawuran Allah

Bangaskiya

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Alkawuran Allah

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

2Bit 3:9Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
2Bit 1:4Ta wurin waɗannan ya ba mu alkawaransa masu girma da kuma masu daraja, domin ta wurinsu ku iya yin tarayya cikin Allahntakarsa, ku kuma kuɓuta daga lalatar da take cikin duniya wadda mugayen sha’awace-sha’awace suke jawowa.
1Kor 10:13Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
Fil 4:19Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
2Kor 1:20Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi suke, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.
1Yoh 1:9In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
Ibr 10:23Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.
Rom 6:23Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
Ibr 6:13Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,
M Sh 31:6Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.