Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Jiran Allah
Bangaskiya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jiran Allah
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (14), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Ish 40:31
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.Zab 27:14
Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.Zab 37:7
Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.Mako 3:25
Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;Ish 30:18
Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!Zab 130:5
Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata.Mik 7:7
Amma game da ni, zan sa bege ga Ubangiji, ina sauraron Allah Mai Cetona; Allahna kuwa zai ji ni.Yaƙ 5:7–8
Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.Zab 33:20
Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.Zab 62:5
Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.Hab 2:3
Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.Zab 37:34
Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.Ish 64:4
Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.Zab 38:15
Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.