Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Kasancewar Allah tare da mu
Bangaskiya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kasancewar Allah tare da mu
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (10), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
Zab 16:11
Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.Fit 33:14
Ubangiji ya amsa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma rage maka nauyin kaya.”Irm 29:13
Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.Zab 27:8
Zuciyata kan faɗa game da kai, “Nemi fuskarsa!” Fuskarka, Ubangiji, zan nema.Zef 3:17
Ubangiji Allahnki yana tare da ke, mai iko ne don ceto. Zai yi matuƙar farin ciki da ke, zai rufe ki da ƙaunarsa, zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”Zab 145:18
Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.Ibr 4:16
Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.Ibr 13:5
Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”Yaƙ 4:8
Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.Mat 1:23
“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.