Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 1 Timoti 4:8

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

1 Timoti 4:8

Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.

Karanta dukan babin: 1 Timoti 4

A cikin mahallinsa

5domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

6In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.

7Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah.

8Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.

9Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa.

10Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

11Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa.

1 Timoti 4

Da Turanci

Berean Standard Bible1 Timothy 4:8For physical exercise is of limited value, but godliness is valuable in every way, holding promise for the present life and for the one to come.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

Mat 6:33Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.
1Tim 6:6Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.
Zab 37:3–4Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
K Mag 19:23Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.
K Mag 22:4Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
Kol 2:21–23“Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”? Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane. Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.
Zab 37:11Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.
Mar 10:30sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi