Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Amon sarkin Yahuda

2Sar 21:19–26 · 2Tar 33:21–25

2 Sarakuna

2Sar 21:19–26

19Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.

20Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi.

21Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu.

22Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.

23Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.

24Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.

25Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

26Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.

2 Tarihi

2Tar 33:21–25

21Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.

22Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.

23Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.

24Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa.

25Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY