Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Manasse sarkin Yahuda

2Sar 21:1–18 · 2Tar 33:1–20

2 Sarakuna

2Sar 21:1–18

1Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba.

2Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

3Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.

4Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.”

5Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari.

6Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.

7Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

8Ba zan ƙara sa Isra’ilawa su fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da na ba wa bawana Musa yă umarce su.”

9Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.

10Ubangiji ya yi magana ta bakin bayinsa annabawa,

11“Manasse, sarkin Yahuda ya aikata waɗannan ƙazantattun zunubai. Ya aikata mugunta fiye da ta Amoriyawan da suka riga shi, ya kuma sa Yahuda ta bauɗe ta wurin yin zunubi saboda gumakansa.

12Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma.

13Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.

14Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su,

15domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”

16Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

17Game da sauran ayyukan mulkin Manasse, da duk abin da ya yi, har da zunubin da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

18Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.

2 Tarihi

2Tar 33:1–20

1Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar.

2Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

3Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada.

4Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.”

5Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari.

6Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.

7Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

8Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.”

9Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.

10Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba.

11Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.

12Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.

13Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.

14Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.

15Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni.

16Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila.

17Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.

18Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila.

19Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba.

20Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY