Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Daga Hezekiya zuwa Yosiya

Yosiya da Littafin Doka

2Sar 22:1–20 · 2Tar 34:1–28

2 Sarakuna

2Sar 22:1–20

1Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.

2Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.

3A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,

4“Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.

5Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,

6wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin.

7Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”

8Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.

9Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”

10Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.

11Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa.

12Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,

13“Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”

14Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

15Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ku faɗa wa mutumin da ya aike ku wurina,

16‘Ga abin da Ubangiji ya ce, zan kawo masifa wa wannan wuri da kuma wa kan mutanen wurin, bisa ga dukan abubuwan da suke a rubuce a cikin littafin da sarkin Yahuda ya karanta.

17Domin sun yashe ni suka ƙona turare wa waɗansu alloli, suka tozarta ni da dukan gumakan da hannuwansu suka sassaƙa, fushina zai yi ƙuna a kan wannan wuri, ba kuwa zai huce ba.’

18Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da kalmomin da ka ji.

19Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

20Saboda haka zan haɗa ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka kuma ba za su ga dukan wannan masifan da zan jawo wa wurin nan ba.’ ” Sai suka kai wa sarki abin da ta faɗa.

2 Tarihi

2Tar 34:1–28

1Yosiya yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara talatin da ɗaya.

2Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin kakansa Dawuda, ba tare da juye dama ko hagu ba.

3A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi.

4A ƙarƙashin umarninsa aka rurrushe bagadan Ba’al, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu, ya farfashe ginshiƙan Ashera da kuma sassaƙaƙƙun siffofi. Ya ragargaza waɗannan kucu-kucu, ya barbaɗa su a kan kaburburan waɗanda suka miƙa musu hadayu.

5Ya ƙone ƙasusuwan firistocin gumaka a kan bagaden da a dā suke miƙa hadayunsu, ta haka ya tsabtacce Yahuda da Urushalima.

6Ya yi haka cikin garuruwan Manasse, Efraim da Simeyon, har zuwa Naftali, da kuma cikin kangwayen kewayensu,

7ya farfashe bagadai da ginshiƙan Ashera; ya niƙa gumaka suka zama gari, ya kuma yayyanka dukan bagadan turare kucu-kucu ko’ina a Isra’ila. Sa’an nan ya koma Urushalima.

8A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya, ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Azaliya da Ma’asehiya mai mulkin birni, tare da Yowa ɗan Yowahaz, marubuci, su gyara haikalin Ubangiji Allah.

9Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima.

10Sa’an nan suka danƙa su ga mutanen da aka naɗa su lura da aiki a kan haikalin Ubangiji. Waɗannan mutane ne suke biyan ma’aikatan da suka gyara suka kuma mai da haikalin.

11Suka kuma ba da kuɗi ga kafintoci da magina don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katakai don yin tsaiko da tankar ginin da sarakunan Yahuda suka bari yă fāɗi ya zama kango.

12Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi,

13sun lura da ma’aikata, suka kuma lura da dukan masu aiki daga aiki zuwa aiki. Waɗansu Lawiyawan su ne marubuta, magatakarda da kuma masu tsaron ƙofofi.

14Yayinda suke fitar da kuɗin da aka kai cikin haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya sami Littafin Dokar Ubangiji da aka bayar ta wurin Musa.

15Hilkiya ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a cikin haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan.

16Sa’an nan Shafan ya ɗauki littafin zuwa wurin sarki, ya faɗa masa, “Manyan ma’aikatanka suna yin kome da aka sa su.

17Mun ɗauke kuɗin da an ajiye a haikalin Ubangiji muka ba wa masu aiki da waɗanda suke lura da su.”

18Sa’an nan Shafan magatakarda ya sanar da sarki ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta daga cikinsa a gaban sarki.

19Da sarki ya ji kalmomin Doka, sai ya yage rigunansa.

20Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.

21Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”

22Hilkiya tare da waɗanda sarki ya aika, suka tafi suka yi magana da annabiya Hulda, wadda take matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai tsaron wurin ajiyar riguna. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.

23Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce faɗa wa mutumin da ya aike ku gare ni,

24‘Ga abin da Ubangiji ya ce zai kawo masifa a wannan wuri da mutanensa, dukan la’anar da aka rubuta a cikin littafin da aka karanta a gaban sarkin Yahuda.

25Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’

26Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yake cewa game da kalmomin da ka ji.

27Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah sa’ad da ka ji abin da ya yi magana a kan wannan wuri da mutanensa, domin kuma ka ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yage rigunanka ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

28Yanzu zan tara ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka ba za su ga dukan masifar da zan kawo a kan wannan wuri da kuma a kan waɗanda suke zama a nan ba.’ ” Sai suka kai amsar wa sarki.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY