Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

A gaban babban firist da Majalisa

Mat 26:57–68 · Mar 14:53–65 · Luk 22:63–71

Mattiyu

Mat 26:57–68

57Waɗanda suka kama Yesu kuwa suka kai shi wurin Kayifas, babban firist, inda malaman dokoki da dattawa suka taru.

58Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

59Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.

60Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,

61suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ”

62Sa’an nan babban firist ya miƙe tsaye, ya ce wa Yesu, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?”

63Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.”

64Sai Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”

65Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.

66Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”

67Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi

68suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”

Markus

Mar 14:53–65

53Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru.

54Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.

55Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.

56Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.

57Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce,

58“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ”

59Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.

60Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?”

61Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”

62Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”

63Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma?

64Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa.

65Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.

Luka

Luk 22:63–71

63Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka.

64Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?”

65Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa.

66Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu.

67Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba,

68in kuma na yi muku tambaya ba za ku iya ba ni amsa ba.

69Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”

70Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amsa ya ce, “Kun faɗa daidai, ni ne.”

71Sai suka ce, “Wace shaida kuma muke nema? Ai, mun ji abin da ya ce da bakinsa.”

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY