Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Shan wahalar Yesu

Littattafan Bishara gefe da gefe · Shan wahalar Yesu

Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu

Mat 26:69–75 · Mar 14:66–72 · Luk 22:54–62 · Yoh 18:25–27

Mattiyu

Mat 26:69–75

69To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”

70Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”

71Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”

72Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”

73Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”

74Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.

75Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.

Markus

Mar 14:66–72

66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.

67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”

68Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.

69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”

70Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”

71Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”

72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu, za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.

Luka

Luk 22:54–62

54Sai suka kama shi suka kai shi gidan babban firist. Bitrus ya bi su daga nesa.

55Amma da suka hura wuta a tsakiyar harabar gidan, kowa ya zauna, sai Bitrus ya zo ya zauna tare da su.

56Wata baiwa ta gan shi zaune kusa da wutar. Ta dube shi sosai sa’an nan, ta ce, “Ai, wannan mutum ma yana tare da shi.”

57Amma ya yi mūsu ya ce, “Mace, ban san shi ba!”

58Bayan ɗan lokaci kaɗan, wani dabam ya gan shi ya ce, “Kai ma ɗayansu ne.” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ba na cikinsu!”

59Bayan kamar sa’a ɗaya, sai wani mutum ya ce, “Ba shakka, mutumin nan ma yana tare da shi, don shi mutumin Galili ne.”

60Bitrus ya amsa ya ce, “Kai, ban ma san abin da kake magana a kai ba!” Yana cikin magana, sai zakara ya yi cara.

61Ubangiji kuma ya juya ya kafa wa Bitrus ido. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Ubangiji ya ce masa, “Kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

62Sai ya fita waje, ya yi kuka mai zafi.

Yohanna

Yoh 18:25–27

25Da Siman Bitrus yana nan tsaye yana jin ɗumin wuta, sai aka tambaye shi, “Kai, kai ma ba ɗaya daga cikin almajiransa ba ne?” Sai ya yi mūsu, yana cewa, “Sam, ba na ciki.”

26Sai wani daga cikin bayin babban firist dangin wanda Bitrus ya sare wa kunne, ya tambaya shi ya ce, “Kana tsammani ban gan ka tare da shi a gonar zaitun ba?”

27Bitrus ya sāke yin mūsu, nan take kuwa zakara ya yi cara.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY