Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › Mafari

Littattafan Bishara gefe da gefe · Mafari

Yohanna Mai Baftisma yana wa’azi

Mat 3:1–12 · Mar 1:1–8 · Luk 3:1–18 · Yoh 1:19–28

Mattiyu

Mat 3:1–12

1A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya

2yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

3Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

4Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.

5Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.

6Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.

7Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.

9Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.

10An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.

11“Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

12Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

Markus

Mar 1:1–8

1Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.

2An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa, “Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka,”

3“muryar mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

4Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.

5Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.

6Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji.

7Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.

8Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

Luka

Luk 3:1–18

1A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.

2A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

3Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.

4Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.

5Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.

6Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

7Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.

9An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”

10Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”

11Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”

12Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”

13Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”

14Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

15Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.

16Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma.

17Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

18Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.

Yohanna

Yoh 1:19–28

19To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.

20Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”

21Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.”

22A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”

23Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”

24To, waɗansu Farisiyawan da aka aika

25suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”

26Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.

27Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”

28Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY