Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Ishaya 43:18–19
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Ishaya 43:18–19
18“Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru; kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
19Duba, ina yi abu sabo! Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba? Ina yin hanya a cikin hamada rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Karanta dukan babin: Ishaya 43
A cikin mahallinsa
15Ni ne Ubangiji, Mai Tsarkin nan, Mahaliccin Isra’ila, Sarkinku.”
16Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya yi hanya ta cikin teku, hanya ta cikin manyan ruwaye,
17wanda ya ja kekunan yaƙi da dawakai, mayaƙa da kuma ƙarin mayaƙa tare ya kwantar da su a can, ba kuwa za su ƙara tashi ba, ya kashe hayaƙi daga lagwani,
18“Ku manta da abubuwan da suka riga suka faru; kada ku yi tunanin abin da ya riga ya wuce.
19Duba, ina yi abu sabo! Yanzu yana faruwa; ba ku gan shi ba? Ina yin hanya a cikin hamada rafuffuka kuma a cikin ƙeƙasasshiyar ƙasa.
20Namun jeji suna girmama ni, diloli da mujiyoyi ma haka, domin na tanada musu ruwa a hamada da rafuffuka a ƙeƙasasshiyar ƙasa, don a ba da abin sha ga mutanena, zaɓaɓɓuna,
21mutanen da na yi saboda kaina don su furta yabona.
22“Duk da haka ba ku kira bisa sunana ba, ya Yaƙub, ba ku gajiyar da kanku saboda ni ba, ya Isra’ila.
Da Turanci
“Do not call to mind the former things; pay no attention to the things of old. Behold, I am about to do something new; even now it is coming. Do you not see it? Indeed, I will make a way in the wilderness and streams in the desert.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Kun riga kun ji waɗannan abubuwa; kuka gan su duka. Ba za ku yarda da su ba? “Daga yanzu zuwa gaba zan faɗa muku sababbin abubuwa, na ɓoyayyun abubuwan da ba ku sani ba.Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.”Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”Zan sa koguna su malalo a ƙeƙasassun tuddai, maɓulɓulan ruwa kuma a kwaruruka. Zan mai da hamada tafkunan ruwa, busasshiyar ƙasa kuma ta zama maɓulɓulan ruwa.“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa. Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada. Yashi mai ƙuna zai zama tafki, ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za tă cika da maɓulɓulan rafuffuka. A mazaunin diloli, inda suka taɓa zama, ciyawa da iwa da kyauro za su yi girma. Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba. Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can, kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi