Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Ishaya 40:31
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Ishaya 40:31
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Karanta dukan babin: Ishaya 40
A cikin mahallinsa
28Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
29Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
30Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
31amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Da Turanci
But those who wait upon the LORD will renew their strength; they will mount up with wings like eagles; they will run and not grow weary, they will walk and not faint.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana.Har yanzu ina da ƙarfin gwiwa a wannan cewa zan ga alherin Ubangiji; a ƙasar masu rai. Ka dogara ga Ubangiji, ka yi ƙarfin hali ka yi ƙarfin zuciya ka kuma dogara ga Ubangiji.Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.Amma ya ce mini, “Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.” Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi