Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › Luka 12:15
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
Luka 12:15
Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”
A cikin mahallinsa
12gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”
13Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.”
14Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?”
15Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”
16Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai.
17Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’
18“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.
Da Turanci
And He said to them, “Watch out! Guard yourselves against every form of greed, for one’s life does not consist in the abundance of his possessions.”Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba. Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki,Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi