Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 1 Korintiyawa 13:4–7

Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK

1 Korintiyawa 13:4–7

4Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.

5Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

6Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.

7Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

Karanta dukan babin: 1 Korintiyawa 13

A cikin mahallinsa

1In ina iya yin magana da harsunan mutane, da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama kamar kuge mai yawan ƙara, ko kuma ƙararrawa mai amo kawai.

2In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne.

3In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

4Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.

5Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.

6Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya.

7Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

8Ƙauna ba ta ƙarewa. Amma in akwai annabci zai shuɗe, harsuna su ɓace, ilimi kuma zai ƙare.

9Gama saninmu ba cikakke ba ne, annabcinmu kuma ba cikakke ba ne.

10Sai dai sa’ad da cikakken ya zo, sai wanda ba cikakke yă shuɗe.

1 Korintiyawa 13

Da Turanci

Berean Standard Bible1 Corinthians 13:4–7Love is patient, love is kind. It does not envy, it does not boast, it is not proud. It is not rude, it is not self-seeking, it is not easily angered, it keeps no account of wrongs. Love takes no pleasure in evil, but rejoices in the truth. It bears all things, believes all things, hopes all things, endures all things.

Nassoshi masu alaƙa

Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.

1Bit 4:8Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
Afi 4:32Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
Gal 5:21–22da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba. Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,
K Mag 10:12Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
Kol 3:12Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa.
Rom 12:9Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.
1Bit 2:24Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.
1Yoh 4:11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna.

Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi