Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Yuni 2027 › Yuni 19
Kalandar Ortodoks · 6 ga Yuni (tsohon lissafi)
Karatun Orthodox na ranar — Yuni 19, 2027
Asabar · Mako na 7 na lokacin Ista · Sauti na 6
Bukukuwa da waliyyai
Asabar ta tunawa da matattu
Azumi
Babu azumi
Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.
Karatun yini
Wasiƙa (domin matattu)
13’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
Wasiƙa
1Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. 2Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. 3Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa. 4Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” 5Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. 6Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne. 7Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. 8Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. 10Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata. 11Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. 12Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. 13Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli. 14A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. 15’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. 16Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa. 17Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. 18Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. 19Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. 20Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.” 21Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. 22Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.” 23Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa, “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya sa’ad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa, 26“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.” 27Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta a zukatansu, su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’ 28“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Al’ummai, za su kuwa saurara!” 30Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. 31Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.
Wasiƙa (domin matattu (wani karatu))
47Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. 48Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. 49Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama. 50Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. 51Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu 52farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. 53Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. 54Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” 55“Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?” 56Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Bishara (domin matattu)
24“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. 25Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. 26Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. 27Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne. 28“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa 29su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. 30Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
Bishara
15Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.” 16Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.” 17Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!” 20Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?” 22Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?” 24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce. 25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
Bishara (domin matattu (wani karatu))
35Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba. 36Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba. 37Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan. 38Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni. 39Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Yuni 6 a kalandar ikilisiya shi ne Yuni 19 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi