Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 15

Kalandar Ortodoks · 2 ga Afirilu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Afirilu 15, 2027

Alhamis · Mako na 5 na Babban Azumi · Sauti na 4

Bukukuwa da waliyyai

Babban Kanon na Waliyyi Andrew na Kirit

Babban Azumi

Azumi: da mai

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Sa’a ta 6

Ish 42:5–16

5Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta. 6“Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci; zan riƙe hannunka. Zan kiyaye ka in kuma sa ka zama alkawari ga mutane haske kuma ga Al’ummai, 7don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu. 8“Ni ne Ubangiji; sunana ke nan! Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka. 9Duba, abubuwan da sun tabbata, sababbin abubuwa kuwa nake furtawa; kafin ma su soma faruwa na sanar da su gare ku.” 10Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu. 11Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu; bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki. Bari mutanen Sela su rera don farin ciki; bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu. 12Bari su ɗaukaka Ubangiji su kuma yi shelar yabonsa a tsibirai. 13Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi, kamar jarumi zai yi himma; da ihu zai tā da kirarin yaƙi zai kuma yi nasara a kan abokan gābansa. 14“Na daɗe ina shiru, na yi shiru na kuma ƙame kaina. Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda, na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki. 15Zan lalatar da duwatsu da tuddai in busar da dukan itatuwansu; zan mai da koguna su zama tsibirai in kuma busar da tafkuna. 16Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba, a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su; zan mai da duhu ya zama haske a gabansu in kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul. Abubuwan da zan yi ke nan; ba zan yashe su ba.

Addu’ar yamma: karatu

Far 18:20–33

20Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai, 21zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.” 22Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji. 23Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? 24Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? 25Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?” 26Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.” 27Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, 28in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.” 29Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.” 30Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.” 31Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.” 32Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.” 33Sa’ad da Ubangiji ya gama magana da Ibrahim, ya tafi, Ibrahim kuma ya koma gida.

Addu’ar yamma: karatu

K Mag 16:17–17:17

17Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa. 18Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa. 19Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai. 20Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji. 21Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni. 22Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye. 23Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni. 24Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa. 25Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa. 26Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba. 27Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna. 28Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa. 29Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau. 30Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan. 31Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci. 32Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane. 33Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne. 17:1Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai. 2Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa. 3Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya. 4Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi. 5Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi. 6Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu. 7Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya! 8Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara. 9Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa. 10Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari. 11Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu. 12Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa. 13In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba. 14Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke. 15Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu. 16Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima? 17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Afirilu 2 a kalandar ikilisiya shi ne Afirilu 15 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi