Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Afirilu 2027 › Afirilu 16

Kalandar Ortodoks · 3 ga Afirilu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Afirilu 16, 2027

Juma’a · Mako na 5 na Babban Azumi · Sauti na 4

Bukukuwa da waliyyai

Venerable Nicetas the Confessor, Abbot of Medikion († 824)

Babban Azumi

Azumi mai tsanani (busasshen abinci: burodi, ganye, ’ya’yan itace)

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Sa’a ta 6

Ish 45:11–17

11“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da ’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana? 12Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama. 13Zan tā da Sairus cikin adalcina. Zan sa dukan hanyoyinsa su miƙe. Zai sāke gina birnina ya kuma ’yantar da mutanena masu bautar talala, amma ba don wata haya ko lada ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.” 14Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kayayyakin Masar da hajar Kush, da waɗannan dogayen Sabenawa, za su ƙetaro zuwa wurinku za su kuma zama naku; za su bi bayanku, suna zuwa cikin sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su roƙe ku, suna cewa, ‘Tabbas Allah yana tare da ku, babu kuma wani; babu wani allah.’ ” 15Tabbatacce kai ne Allah wanda ya ɓoye kanka, Ya Allah da Mai Ceton Isra’ila. 16Dukan masu yin gumaka za su sha kunya; za su fita da kunya gaba ɗaya. 17Amma Ubangiji zai ceci Isra’ila da madawwamin ceto; ba za ku sāke shan kunya ko ƙasƙanci ba, har abada.

Addu’ar yamma: karatu

Far 22:1–18

1Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” 2Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.” 3Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa. 4A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa. 5Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.” 6Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya, 7sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” 8Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya. 9Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. 10Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. 11Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” 12Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.” 13Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa. 14Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.” 15Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu 16ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba, 17tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu, 18ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”

Addu’ar yamma: karatu

K Mag 17:17–18:5

17Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi. 18Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci. 19Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka. 20Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala. 21Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa. 22Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa. 23Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci. 24Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya. 25Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi. 26Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu. 27Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne. 28Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa. 18:1Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai. 2Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa. 3Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo. 4Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu. 5Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Afirilu 3 a kalandar ikilisiya shi ne Afirilu 16 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi