Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Faɗuwar Urushalima

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Faɗuwar Urushalima

An saki Yehohiyacin

2Sar 25:27–30 · Irm 52:31–34

2 Sarakuna

2Sar 25:27–30

27A shekara ta talatin da bakwai ta bautar Yehohiyacin sarkin Yahuda, a shekaran da Ewil-Merodak ya ci sarautan Babilon, sai ya saki Yehohiyacin daga jaru, ya sake shi a rana ashirin da bakwai ga watan goma sha biyu.

28Ya yi wa Yehohiyacin maganar alheri, ya kuma ɗaukaka shi sama da sauran sarakunan da suke tare da shi a Babilon.

29Don haka Yehohiyacin ya tuɓe kayan fursuna. Kowace rana kuwa yakan ci abinci a teburin sarki har iyakar ransa.

30Sarki kuma ya yanka masa kuɗin da za a dinga ba shi, kowace rana muddin ransa.

Irmiya

Irm 52:31–34

31A shekarar da Ewil-Merodak ya zama Sarkin Babilon, sai ya nuna wa Yehohiyacin Sarkin Yahuda alheri. Ya fisshe shi daga kurkuku. Wannan ya faru ran ashirin da biyar ga watan goma sha biyu a shekara ta talatin da bakwai bayan da aka kai Yehohiyacin bauta.

32Ewil-Merodak ya nuna wa Yehohiyacin alheri, ya ba shi matsayi na daraja fiye da waɗansu sarakunan da aka kai su bautar talala a Babilon tare da shi.

33Yehohiyacin ya tuɓe tufafin kurkuku, ya riƙa cin abinci kullum a teburin sarki, har dukan sauran kwanakin ransa.

34Kowace rana akan ba shi kyauta bisa ga umarnin sarkin Babilon, saboda bukatarsa. Haka aka yi masa har rasuwarsa.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY