Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Faɗuwar Urushalima

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Faɗuwar Urushalima

Zedekiya da faɗuwar Urushalima

2Sar 24:18–20; 25:1–21 · 2Tar 36:11–21 · Irm 52:1–27

2 Sarakuna

2Sar 24:18–20; 25:1–21

24:18Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna.

24:19Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi.

24:20Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.

25:1A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.

25:2Haka birnin ta kasance a kewaye har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.

25:3A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci.

25:4Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba.

25:5Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse.

25:6Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

25:7Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon.

25:8A rana ta bakwai na watan biyar, wadda ta zama shekara ta goma sha tara ta mulkin Sarki Nebukadnezzar na Babilon, Nebuzaradan, babban hafsan matsaran sarki, kuma bafadan sarkin Babilon, ya zo Urushalima

25:9Ya cinna wa haikalin Ubangiji wuta, da fadan sarki, da kuma dukan gidajen Urushalima. Ya kuma ƙone duk wani gini mai muhimmanci.

25:10Dukan mayaƙan Babilon a ƙarƙashin umarnin babban hafsan matsaran sarki, suka rushe katangar Urushalima.

25:11Nebuzaradan babban hafsan matsaran, ya kwashi waɗanda suka rage a cikin birnin, tare da sauran jama’a, da waɗanda suka miƙa kansu ga sarkin Babilon, ya kai su bauta.

25:12Amma hafsan ya bar waɗansu daga cikin mafiya talauci na ƙasar don su yi aiki a lambunan inabi da kuma gonaki.

25:13Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.

25:14Suka ɗauke tukwane, da manyan cokula, da acibalbal, da kwanoni, da dai dukan kayan da aka yi da tagulla don hidima a haikalin Ubangiji.

25:15Babban hafsan matsaran sarkin ya kwashe har da kwanoni na kwashe garwashin wuta da sauran kwanoni, dukansu kuwa ƙeran zinariya ko azurfa tsatsa ne.

25:16Tagullar ginshiƙai biyun nan, da ta ƙaton kwanon da ake ce da shi Teku, da ta dukan amalanke masu riƙe ruwa waɗanda Sarki Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji, sun fi gaba a auna su.

25:17Tsawon kowane ginshiƙi, ƙafa ashirin da bakwai ne. Hulunan tagullan da suke ƙwalƙwalin kowane ginshiƙi kuma yana da tsawon ƙafa huɗu da rabi. Kuma aka yi masa ado da saƙa da ’ya’yan itace kewaye da shi. Bayan ginshiƙin ma haka yake.

25:18Babban hafsan ya kwashi Serahiya babban firist, da Zefaniya na biye da shi a girma, da matsara ƙofofi uku.

25:19Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin.

25:20Nebuzaradan, babban hafsan, ya kwashe su duka ya kawo su wurin sarkin Babilon a Ribla.

25:21A can Ribla, a ƙasar Hamat, sarkin Babilon ya sa aka kashe su. Haka Yahuda ta tafi bauta daga ƙasarta.

2 Tarihi

2Tar 36:11–21

11Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya.

12Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.

13Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.

14Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.

15Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.

16Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.

17Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.

18Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.

19Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.

20Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.

21Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.

Irmiya

Irm 52:1–27

1Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Sunan uwarsa Hamutal, ’yar Irmiya, wanda yake zaune a Libna.

2Sarki Zedekiya ya aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda Sarki Yehohiyakim ya yi.

3Al’amarin ya zama da muni ƙwarai a cikin Isra’ila da Yahuda, don haka Ubangiji ya husata har ya sa aka kai mutanen bautar talala. Zedekiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babilon.

4A kan rana ta goma ga watan goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya, Sarkin Yahuda, sai Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, ya zo yaƙi da Urushalima tare da dukan sojojinsa. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina katanga kewaye da ita.

5An kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.

6A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.

7Sai aka huda katangan birnin, sojojin kuwa suka gudu, suka fita daga cikin birnin da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu, kusa da gonar sarki, sa’ad da Babiloniyawa suke kewaye da birnin. Sojojin suka nufi wajen Araba.

8Amma sojojin Babiloniyawa suka runtumi sarki Zedekiya, suka ci masa a filayen Yeriko. Dukan sojoji suka yashe shi.

9Da aka kama Zedekiya, sai aka kai shi wurin Sarkin Babilon a Ribla a ƙasar Hamat, a nan ne Sarkin Babilon ya yanke masa shari’a.

10Sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idonsa. Ya kuma kashe dukan shugabannin Yahuda a Ribla.

11Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya, ya kuma sa masa ƙuƙumi, aka kai shi Babilon inda aka sa shi a kurkuku har ran da ya mutu.

12A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.

13Sai ya ƙone haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gine-gine masu alfarman da suke Urushalima.

14Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.

15Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.

16Amma ya bar waɗansu matalauta na gaske a ƙasar don su yi aiki a gonakin inabi, da sauran gonaki.

17Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon.

18Suka kwashe tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da hantsuka, da daruna, da tasoshin ƙona turare, da kayayyakin tagulla waɗanda ake amfani da su domin hidimar haikali.

19Suka kuma kwashe ƙananan kwanonin sha, da farantan wuta, da daruna, da tukwane, da alkukai, da tasoshin ƙona turare, da kwanonin miƙa hadayar sha. Duk abin da yake na zinariya da azurfa, shugaban matsara ya kwashe.

20Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.

21Tsawon kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne, kewayensa kuwa kamu goma sha biyu ne, kaurinsa kuma huɗu ne. Kowannensu yana da rami a ciki.

22A kan kowane ginshiƙi, an yi masa dajiyar tagulla, tsayinta kamu biyar. A bisa kan kowace dajiya akwai raga da siffofin rumman na tagulla kewaye da dajiyar. Ginshiƙi na biyu ma haka yake da siffofin rumman.

23Akwai siffofin rumman tasa’in da shida da ake gani a gefen. Dukan siffofin rumman da suke a kan ragar kewaye, guda ɗari ne.

24Shugaban matsara kuma ya ɗauki Serahiya babban firist, da Zefaniya wanda yake biye da babban firist, da mutum uku masu tsaron ƙofar, ya tafi da su.

25Daga cikin birnin kuma ya ɗauki shugaban sojojin, da mutum bakwai ’yan majalisar sarki, da magatakardan shugaban sojojin wanda yakan tara sojojin ƙasar, da mutane sittin na ƙasar, waɗanda aka same su a birnin, ya tafi da su.

26Nebuzaradan shugaban matsara ya tafi da waɗannan mutane wurin Sarkin Babilon a Ribla,

27Sarkin Babilon kuwa ya kashe su a Ribla a ƙasar Hamat. Haka aka tafi da mutanen Yahuda bautar talala, daga ƙasarta.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY