Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Ataliya da yaron nan Yowash

2Sar 11:1–21 · 2Tar 22:10–12; 23:1–21

2 Sarakuna

2Sar 11:1–21

1Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.

2Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.

3Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.

4A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.

5Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,

6kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan ’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,

7ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.

8Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”

9Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.

10Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.

11Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.

12Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”

13Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji.

14Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”

15Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.”

16Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta.

17Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane.

18Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji.

19Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta,

20dukan mutanen ƙasar suka yi murna. Birnin ya sami salama don an kashe Ataliya da takobi a fada.

21Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki.

2 Tarihi

2Tar 22:10–12; 23:1–21

22:10Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan ’yan gidan sarautar Yahuda.

22:11Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin ’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba ’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita ’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi.

22:12Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.

23:1A shekara ta bakwai Yehohiyada ya nuna ƙarfinsa. Ya yi alkawari da shugabanni na ɗari-ɗari, Azariya ɗan Yeroham, Ishmayel ɗan Yehohanan, Azariya ɗan Obed, Ma’asehiya ɗan Adahiya, da Elishafat ɗan Zikri.

23:2Suka ratsa cikin Yahuda suka tattara Lawiyawa da shugabannin iyalan Isra’ilawa daga dukan garuruwa. Sa’ad da suka zo Urushalima,

23:3dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.

23:4Yanzu ga abin da za ku yi, shi ne, kashi ɗaya bisa uku na firistoci da Lawiyawa waɗanda za su yi aiki a Asabbaci su yi tsaro a ƙofofi,

23:5kashi ɗaya bisa ukunku a fadan sarki, kashi ɗaya bisa uku kuma, a Ƙofar Harsashi, sai kuma dukan sauran mutane su kasance a filayen haikalin Ubangiji.

23:6Babu wanda zai shiga haikalin Ubangiji sai firistoci da Lawiyawan da suke a aiki; za su iya shiga domin su tsarkaku ne, amma sauran mutane za su kiyaye abin da Ubangiji ya sa su yi.

23:7Lawiyawa za su tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makamansa a hannunsa. Duk wanda ya shiga haikali sai a kashe shi. Ku tsaya kusa da sarki a duk inda ya tafi.”

23:8Lawiyawa da dukan mutanen Yahuda suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa, waɗanda suke aiki a Asabbaci da waɗanda suka gama aiki, gama Yehohiyada firist bai bar waɗansu ɓangarori ba.

23:9Sa’an nan ya ba shugabannin māsu da garkuwoyi manya da ƙanana na sarki Dawuda, waɗanda suke cikin haikalin Allah.

23:10Ya kuma sa dukan mutane, kowanne da makaminsa a hannunsa, kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikali.

23:11Yehohiyada da ’ya’yansa maza suka fitar da ɗan sarki suka sa rawani a kansa; suka miƙa masa alkawarin, suka kuma yi shelarsa a matsayin sarki. Suka shafe shi suka kuma tā da murya suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”

23:12Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji.

23:13Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”

23:14Yehohiyada firist ya fito da shugabanni waɗanda suke shugabancin rundunar sojoji, ya ce musu, “Ku fitar da ita tsakanin sojoji ku kuma kashe duk wanda ya bi ta da takobi.” Gama firist ya ce, “Kada ku kashe ta a haikalin Ubangiji.”

23:15Saboda haka suka kama ta yayinda take kaiwa mashigin Ƙofar Doki a filin fada, a can suka kashe ta.

23:16Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji.

23:17Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan.

23:18Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.

23:19Ya kuma sa matsaran ƙofofi a ƙofofin haikalin Ubangiji don kada wani da ba shi da tsarki yă shiga.

23:20Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, manyan gari, shugabannin mutane da dukan mutanen ƙasar tare da shi ya saukar da sarki daga haikalin Ubangiji. Suka shiga fada ta Ƙofar Bisa suka kuma zaunar da sarki a kujerar sarauta,

23:21sai dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki. Birnin kuwa ya samu zaman lafiya domin an kashe Ataliya da takobi.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY