Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Yowash ya gyara haikali

2Sar 12:1–16 · 2Tar 24:1–14

2 Sarakuna

2Sar 12:1–16

1A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba.

2Yowash ya aikata abin da yake daidai a idon Ubangiji domin Yehohiyada firist ya koya masa.

3Amma fa ba a kawar da masujadan kan tuddai ba; mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da kuma ƙona turare a kan tuddai.

4Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali.

5Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.”

6Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba.

7Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.”

8Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba.

9Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin.

10Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.

11Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,

12masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.

13Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin Ubangiji ba;

14an ba ma’aikatan da suka gyara haikalin ne.

15Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci.

16Ba a kawo kuɗi daga hadayun laifi da na hadayun zunubi a haikalin Ubangiji ba, waɗannan na firistoci ne.

2 Tarihi

2Tar 24:1–14

1Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba.

2Yowash ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji duka shekarun Yehohiyada firist.

3Yehohiyada ya zaɓi mata biyu dominsa, yana kuma da ’ya’ya maza da ’ya’ya mata.

4Wani lokaci daga baya Yowash ya yanke shawara yă gyara haikalin Ubangiji.

5Ya tara firistoci da Lawiyawa wuri ɗaya ya ce musu, “Ku je garuruwan Yahuda ku karɓa kuɗin da ya kamata a biya shekara-shekara daga dukan Isra’ila, don gyaran haikalin Allahnku. Ku yi haka yanzu.” Amma Lawiyawa ba su yi haka nan da nan ba.

6Saboda haka sarki ya kira Yehohiyada babban firist ya ce masa, “Me ya sa ba ka bukaci Lawiyawa su kawo harajin da Musa bawan Ubangiji ya ce a biya daga Yahuda da Urushalima da kuma taron Isra’ila domin Tentin Sujada Shaida ba?”

7Yanzu ’ya’ya muguwar macen nan Ataliya maza sun fasa zuwa cikin haikalin Allah, suka kuma yi amfani da kayayyaki masu tsarki ma wa Ba’al.

8Bisa ga umarnin sarki, aka yi akwati aka sa a waje, a mashigin haikalin Ubangiji.

9Aka yi umarni a Yahuda da Urushalima cewa ya kamata suka kawo wa Ubangiji harajin da Musa bawan Allah ya bukaci daga Isra’ila a hamada.

10Dukan hafsoshi da dukan mutane suka kawo nasu kuɗin da aka sa musu da farin ciki, suna zuba su cikin akwatin sai da ya cika.

11Duk sa’ad da Lawiyawa suka fito da akwatin zuwa ga hafsoshin sarki, suka kuma ga cewa akwatin yana da kuɗi mai yawa, sai magatakardan fada da hafsan babban firist su zo su juya kuɗin daga akwatin su mai da shi wurinsa. Sun riƙa yin haka kullum suka tara kuɗi mai yawa.

12Sarki da Yehohiyada suka ba da shi ga mutanen da suka yi aikin da ake bukata don haikalin Ubangiji. Suka ɗauki masu gini da kafintoci don su gyara haikalin Ubangiji, da kuma ma’aikatan ƙarafa da tagulla don su gyara haikalin.

13Mutanen da suke lura da aikin natsattsu ne, kuma gyare-gyaren suka ci gaba a ƙarƙashinsu. Suka sāke gina haikalin Allah bisa ga ainihin fasalinsa suka ƙara masa ƙarfi.

14Da suka gama, suka kawo sauran kuɗin wa sarki da Yehohiyada, da su ne kuwa aka yi kayayyaki domin hidima da kuma domin hadayun ƙonawa, haka kuma kwanoni da sauran kayayyakin zinariya da azurfa. Muddin Yehohiyada yana raye, aka riƙa kawo hadayun ƙonawa a haikalin Ubangiji.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY