Bible Explorer

Bincika › Sarakuna da Tarihi gefe da gefe › Sarakunan Yahuda

Sarakuna da Tarihi gefe da gefe · Sarakunan Yahuda

Ahaziya sarkin Yahuda

2Sar 8:25–29 · 2Tar 22:1–6

2 Sarakuna

2Sar 8:25–29

25A shekara ta goma sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya fara mulki.

26Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri, sarkin Isra’ila.

27Ya bi gurbin gidan Ahab, ya yi mugunta a gaban Ubangiji yadda gida Ahab ta yi, gama yana da dangantaka ta aure da gidan Ahab.

28Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;

29saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

2 Tarihi

2Tar 22:1–6

1Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.

2Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.

3Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.

4Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

5Ya kuma bi shawararsu sa’ad da ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab sarkin Isra’ila don yă yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Sai Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;

6saboda haka ya dawo Yezireyel don yă yi jinyar raunin da suka yi masa a Rama cikin yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sa’an nan Azariya ɗan Yehoram sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel don yă ga Yoram ɗan Ahab domin ya ji rauni.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY