Bible Explorer

Bincika › Littattafan Bishara gefe da gefe › A Urushalima

Littattafan Bishara gefe da gefe · A Urushalima

Misalin manoman gonar inabi

Mat 21:33–46 · Mar 12:1–12 · Luk 20:9–19

Mattiyu

Mat 21:33–46

33“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.

34Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.

35“Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.

36Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.

37A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’

38“Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’

39Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.

40“To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?”

41Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”

42Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?

43“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.

44Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”

45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.

46Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

Markus

Mar 12:1–12

1Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.

2Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu.

3Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.

4Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.

5Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

6“Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’

7“Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’

8Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.

9“To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin.

10Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.

11Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?”

12Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.

Luka

Luk 20:9–19

9Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.

10A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.

11Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.

12Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.

13“Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’

14“Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’

15Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi. “To, me mai gonar inabin zai yi da su?

16Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”

17Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’

18Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”

19Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.

An yi alama: kalmomin da kowane labari yake da su, a fassarar da kuke karantawa. Kalmomin da suka fi yawa (“da”, “ya”) ba a yi musu alama ba; kalma a wani salo dabam wataƙila ba za a yi mata alama ba.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · An zaɓi sassa masu kama da juna da hannu daga rubutun, an kuma duba su da ayoyi masu alaƙa na OpenBible.info (CC BY). Abu ɗaya ko magana ɗaya kawai ake sa gefe da gefe. OpenBible.info · CC BY