Bible Explorer

Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Godiya

Motsin zuciya

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Godiya

Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.

1Tes 5:18ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
Afi 5:20Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
Kol 3:15Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
Zab 107:1Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Zab 106:1Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
Yaƙ 1:17Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Zab 100:4Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
Fil 4:6Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.
Kol 3:17Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.
Kol 4:2Ku nace da yin addu’a, kuna zaman tsaro da kuma godiya.
Zab 118:24Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
Zab 136:1Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.
1Tar 16:34Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.
Zab 69:30Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.
Zab 28:7Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.

Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.

Tushe

Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.