Gida › Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce › Kishi da hassada
Motsin zuciya
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Kishi da hassada
Ayoyin da masu karatu suka fi komawa gare su don wannan jigo (15), an ambace su gaba ɗaya daga Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa.
K Mag 14:30
Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.Yaƙ 3:16
Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.K Mag 27:4
Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?Gal 5:19–21
Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.1Kor 3:3
Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba?1Kor 13:4
Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai.Yaƙ 3:14
Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya.Fit 20:17
Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”Yaƙ 4:2–3
Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.Ayu 5:2
Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci.M Had 4:4
Sai na gane cewa, duk wata fama da duk wata nasara sun samo asali daga kishin da mutum yake yi na maƙwabcinsa ne. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.K Mag 23:17
Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.Ayy M 7:9
“Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shiGal 5:26
Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna.1Bit 2:1
Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna.Waɗannan ayoyi ne da masu karatu suka fi komawa a wannan batu — ba koyarwa a kansa ba. Karanta kowanne a cikin surarsa.
Tushe
Ayoyin kowane jigo da tsarinsu: bayanan jigogi na OpenBible.info, bisa ƙuri’un masu karatu: OpenBible.info · CC BY 4.0
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible.