Gida › Shahararrun ayoyin Littafi Mai Tsarki › 2 Timoti 2:15
Ayar Littafi Mai Tsarki · SRK
2 Timoti 2:15
Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
Karanta dukan babin: 2 Timoti 2
A cikin mahallinsa
12in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;
13in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”
14Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.
15Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai.
16Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.
17Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus,
18waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu.
Da Turanci
Make every effort to present yourself approved to God, an unashamed workman who accurately handles the word of truth.Nassoshi masu alaƙa
Sassan da masu karatu suka fi danganta wa da wannan.
A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba,In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi.Ai, ba mai yabon kansa ake amincewa da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba.Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kuna zuba ido ga wannan, sai ku yi matuƙar ƙoƙari don a same ku ba tabo, sai dai zaman salama da shi.Tushe: OpenBible.info, CC BY 4.0 · Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi