Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 21

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Mayu 21, 2027

Juma’a · Mako na 7 na lokacin yau da kullum

Bukukuwa da waliyyai

Juma’a a mako na 7 na lokacin yau da kullum

Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore

Waliyyi Christopher Magallanes, firist, da abokansa, shahidai · Tunawa da ba dole ba

Azumi da tuba

Ranar tuba

Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.

Karatun yini

Karatu na farko

Ba ya cikin wannan fassara

Zaburar amsawa

Zab 119:12, 16, 18, 27, 34–35

12Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka. 16Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba. 18Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka. 27Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka. 34Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata. 35Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.

Bishara

Mar 10:1–12

1Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba. 2Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?” 3Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?” 4Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.” 5Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’ 7‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’ Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.” 10Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. 11Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Tsarkakan ranar

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi