Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 21

Kalandar Ortodoks · 8 ga Mayu (tsohon lissafi)

Karatun Orthodox na ranar — Mayu 21, 2027

Juma’a · Mako na 3 na lokacin Ista · Sauti na 2

Bukukuwa da waliyyai

Holy Apostle and Evangelist John the Theologian († 98-117)

Ranar azumi

Ana iya cin kifi

Wannan yana bin dokar gidan zuhudu. A cikin ikkilisiya, ana tsara gwargwadon azumi tare da mai sauraron furcin zunubi, bisa ga lafiya, shekaru da yanayi.

Karatun yini

Addu’ar yamma: karatu

1Yoh 3:21–4:6

21Abokaina ƙaunatattu, in zukatanmu ba su ba mu laifi ba, muna da ƙarfin halin tsayawa a gaban Allah ke nan. 22Muna kuma samun dukan abin da muka roƙa daga gare shi, domin muna biyayya da umarnansa, muna kuma yin abin da ya gamshe shi. 23Umarninsa kuwa shi ne, mu gaskata da sunan Ɗansa, Yesu Kiristi, mu kuma ƙaunaci juna kamar yadda ya umarce mu. 24Waɗanda suke biyayya da umarnansa kuwa suna rayuwa a cikinsa, shi kuma a cikinsu. Ta haka muka san cewa yana raye a cikinmu. Mun san haka ta wurin Ruhun da ya ba mu. 4:1Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. 2Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. 3Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya. 4Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. 5Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. 6Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

Addu’ar yamma: karatu

1Yoh 4:11–16

11Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. 12Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan. 13Mun san cewa muna rayuwa a cikinsa shi kuma a cikinmu, domin ya ba mu Ruhunsa. 14Mun gani, mun kuma shaida cewa Uba ya aiko Ɗansa domin yă zama Mai Ceton duniya. 15Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.

Addu’ar yamma: karatu

1Yoh 4:20–5:5

20Duk wanda ya ce, “Ina ƙaunar Allah,” amma yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne. Gama duk wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa da yake gani, ba zai iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba. 21Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa. 5:1Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

Addu’ar asuba: Bishara

Yoh 21:15–25

15Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.” 16Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.” 17Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina. 18Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.” 19Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!” 20Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”) 21Da Bitrus ya gan shi sai ya ce, “Ubangiji, wannan fa?” 22Yesu ya amsa ya ce, “Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.” 23Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, “In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?” 24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce. 25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.

Wasiƙa

Ayy M 8:40–9:19

40Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya. 9:1Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist 2ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima. 3Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. 4Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?” 5Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, “Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa. 6Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.” 7Mutanen da suke tafiya tare da Shawulu suka rasa bakin magana; sun ji muryar amma ba su ga kowa ba. 8Shawulu ya tashi daga ƙasa, amma sa’ad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus. 9Kwana uku yana a makance, bai ci ba bai kuma sha kome ba. 10A Damaskus kuwa akwai wani almajiri mai suna Ananiyas. Ubangiji ya kira shi a cikin wahayi ya ce, “Ananiyas!” Ananiyas ya amsa, “Ga ni, ya Ubangiji.” 11Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a. 12Cikin wahayi ya ga wani mutum mai suna Ananiyas ya zo ya sa hannuwansa a kansa don yă sāke samun ganin gari.” 13Ananiyas ya amsa ya ce, “Ubangiji, na ji labarin mutumin nan sosai da kuma duk lahanin da ya yi wa tsarkakanka a Urushalima. 14Ga shi kuma ya zo nan da izinin manyan firistoci, don yă kama duk wanda yake kiran bisa sunanka.” 15Amma Ubangiji ya ce wa Ananiyas, “Je ka! Wannan mutum zaɓaɓɓen kayan aikina ne don yă kai sunana a gaban Al’ummai da sarakunansu da kuma a gaban mutanen Isra’ila. 16Zan nuna masa wahalar da dole zai sha saboda sunana.” 17Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.” 18Nan da nan, sai wani abu kamar ɓawo ya fāɗo daga idanun Shawulu, ya kuma sāke iya ganin gari. Sai ya tashi aka kuma yi masa baftisma, 19bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.

Wasiƙa (domin Waliyyi Yohanna)

1Yoh 1:1–7

1Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai. 2Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. 3Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi. 4Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yă zama cikakke. 5Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.

Bishara

Yoh 6:48–54

48Ni ne burodin rai. 49Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu. 50Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba. 51Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.” 52Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?” 53Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba. 54Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.

Bishara (domin Waliyyi Yohanna)

Yoh 19:25–27; 21:24–25

25To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” 27ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa. 21:24Wannan shi ne almajirin da ya ba da shaida a kan waɗannan abubuwa ya kuma rubuta su. Mun san cewa shaidarsa gaskiya ce. 25Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.

Kwanakin suna bin kalandar Julian ta Ikilisiyar Rasha (kamar Ikilisiyoyin Serbia da Georgia da Dutsen Athos): Mayu 8 a kalandar ikilisiya shi ne Mayu 21 a kalandar gari. Ikilisiyoyin da ke amfani da sabuwar kalanda (Girka, Romania, Bulgaria, Ukraine…) suna yin bukukuwan da ba sa canzawa da na tsarkaka a ainihin ranar gari, kwanaki 13 kafin haka, kuma wasu karatunsu sun bambanta; Ista da kwanakin da suka dogara da ita iri ɗaya ne.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi