Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 22
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Mayu 22, 2027
Asabar · Mako na 7 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Asabar a mako na 7 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyya Rita ta Cascia, mai zuhudu · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
13Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin ’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa; 14gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne. 15Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; 16iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake. 17Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu, 18tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
Bishara
13Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. 14Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 15Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 16Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.
Tsarkakan ranar
- Waliyya Rita ta Cascia, mai zuhudu
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi