Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Mayu 2027 › Mayu 20
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Mayu 20, 2027
Alhamis · Mako na 7 na lokacin yau da kullum
Bukukuwa da waliyyai
Alhamis a mako na 7 na lokacin yau da kullum
Tunawa da ba dole ba · Launin ibada: kore
Waliyyi Bernardine na Siena, firist · Tunawa da ba dole ba
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
1Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a. 2Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana. 3Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara. 4Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa. 6Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.
Bishara
41Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba. 42“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku. 43In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu. 45In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu. 47In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu, 48inda “ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a iya kashewa.’ 49Za a tsarkake kowa da wuta. 50“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
Tsarkakan ranar
- Waliyyi Bernardine na Siena, firist
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi