Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 11

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Maris 11, 2027

Alhamis · Mako na 4 na lokacin Azumi

Bukukuwa da waliyyai

Alhamis a mako na 4 na lokacin Azumi

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Fit 32:7–14

7Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama mutanenka, waɗanda ka fitar da su daga Masar sun ƙazantu. 8Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.” 9Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.” 10Yanzu ka bar ni kurum fushina yă yi ƙuna a kansu, in hallaka su. Sa’an nan in maishe ka al’umma mai girma. 11Amma Musa ya nemi tagomashin Ubangiji, Allahnsa ya ce, “Ya Ubangiji don me fushinka zai yi ƙuna a kan mutanenka, waɗanda ka fisshe su daga Masar da ikon hannunka mai girma? 12Don me za ka sa Masarawa su ce, ‘Ai, da mugun nufi ne ya fito da su don yă shafe su daga fuskar duniya’? Ka juya daga fushinka mai zafi, ka ji tausayi, kada ka kawo masifa a kan mutanenka. 13Ka tuna da bayinka Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, waɗanda ka rantse da kanka cewa, ‘Zan mai da zuriyarka kamar taurarin sama kuma zan ba wa zuriyarka wannan ƙasa wadda na yi musu alkawari, za tă kuma zama abin gādonsu har abada.’ ” 14Sai Ubangiji ya yi juyayi, bai kuwa kawo wa mutanensa bala’in da ya yi niyya ba.

Zaburar amsawa

Zab 106:19–23

19A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada. 20Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa. 21Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar, 22mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku. 23Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.

Bishara

Yoh 5:31–47

31“In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. 32Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce. 33“Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. 34Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci. 36“Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. 37Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, 38maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, 40duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai. 41“Ni ba na neman yabon mutane, 42na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. 43Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. 44Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici? 45“Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. 47Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi