Bible Explorer Samu manhajar

Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 10

Kalandar Katolika

Karatun Mass (Katolika) — Maris 10, 2027

Laraba · Mako na 4 na lokacin Azumi

Bukukuwa da waliyyai

Laraba a mako na 4 na lokacin Azumi

Ranar mako · Launin ibada: shunayya

Karatun yini

Karatu na farko

Ish 49:8–15

8Ga abin da Ubangiji yana cewa, “A lokacin tagomashina zan amsa muku, kuma a ranar ceto zan taimake ku; zan kiyaye ku zan kuma sa ku zama alkawari ga mutane, don ku maido da ƙasa ku kuma sāke raba gādon kufai, 9don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’ ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku ’yantu!’ “Za su yi kiwo kusa da hanyoyi su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu. 10Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa. 11Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi, a kuma gyara manyan hanyoyina. 12Duba, za su zo daga nesa waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma, waɗansu daga yankin Aswan.” 13Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala. 14Amma Sihiyona ta ce, “ Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.” 15“Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!

Zaburar amsawa

Zab 145:8–9, 13–14, 17–18

8Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna. 9Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi. 13Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi. 14Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa. 17Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi. 18Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

Bishara

Yoh 5:17–30

17Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” 18Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah. 19Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. 20Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. 21Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. 22Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, 23don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan. 24“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. 25Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. 26Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. 27Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne. 28“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa 29su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. 30Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.

Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.

Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi