Gida › Karatun Littafi Mai Tsarki na kowace rana › Maris 2027 › Maris 12
Kalandar Katolika
Karatun Mass (Katolika) — Maris 12, 2027
Juma’a · Mako na 4 na lokacin Azumi
Bukukuwa da waliyyai
Juma’a a mako na 4 na lokacin Azumi
Ranar mako · Launin ibada: shunayya
Azumi da tuba
Kamewa daga nama
Kowace Juma’a ranar tuba ce; kowace taron bishop-bishop yana tsara yadda ake kiyaye ta: kamewa daga nama ko wani aikin tuba. Azumi ya wajaba daga shekara 18 zuwa 59, kamewa daga shekara 14.
Karatun yini
Karatu na farko
Ba ya cikin wannan fassara
Zaburar amsawa
16fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. 17Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. 18Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. 19Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu; 20yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye. 22Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
Bishara
1Bayan wannan, sai Yesu ya yi ta zagawa a cikin Galili, da ganga bai yarda yă je Yahudiya ba domin Yahudawa a can suna nema su kashe shi. 2Amma sa’ad da Bikin Tabanakul na Yahudawa ya yi kusa, 10Amma fa, bayan ’yan’uwansa suka tafi Bikin, shi ma ya tafi, ba a fili ba, amma a ɓoye. 25A nan ne fa waɗansu mutane daga Urushalima suka fara tambaya suna cewa, “Ashe, ba wannan mutum ne suke nema su kashe ba? 26Ga shi nan yana magana a fili, su kuma ba su ce masa uffam ba. Ko hukumomi sun yarda cewa shi ne Kiristi? 27Mun dai san inda mutumin nan ya fito; amma sa’ad da Kiristi ya zo ba wanda zai san inda ya fito.” 28Yesu yana cikin koyarwa a filin haikali ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “I, kun san ni, kun kuma san inda na fito. Ban zo don kaina ba, sai dai shi da ya aiko ni mai gaskiya ne. Ba ku san shi ba, 29amma na san shi, domin ni daga wurinsa ne, kuma shi ya aiko ni.” 30Da jin haka, sai suka yi ƙoƙari su kama shi, sai dai ba wanda ya taɓa shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.
Kalandar Roma ta gama-gari; taron bishop-bishop na iya mayar da wasu bukukuwa (Bayyanuwar Ubangiji, Hawan Yesu Sama, Jiki da Jinin Kristi) zuwa ranar Lahadi ko ƙara nasu. Littafin karatu: zagayen Lahadi B, shekarar ranakun mako I.
Tushe: Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa · © 2009, 2020 Biblica, Inc., CC BY-SA 4.0; changed: footnotes, headings and the letters over Psalm 119 left out, verses in the app's numbering. The original work by Biblica, Inc. is available for free at www.biblica.com and open.bible. · Tushe da haƙƙoƙi